BBC navigation

'Yan sanda a Thailand sun farma masu bore

An sabunta: 24 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:48 GMT

Zanga-zanga a Bangkok, Thailand

'Yan Sanda a Bangkok babban birnin kasar Thailand sun harba hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zanga wadanda suka hallara a wani babban taron gangami na nuna adawa da gwamnatin Ying-Luck Shinwatra.

Masu zanga-zangar sun zarge ta da zama 'yar amshin shatan dan uwan ta Taskin Shinawatra.

Dan uwan nata Taskin Shinawatra tsohon Prime Minista ne mai wuyar sha'ani wanda aka hambarar a shekara ta dubu biyu da shida.

Ying-Luck Shinwatra ta zargi masu boren da yunkurin hambar da ita.

Akwai fargabar da ake da ita cewar boren da za a yi a yau Asabar zai tada hatsaniya bayan an dan samu kwanciyar hankali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.