BBC navigation

An kammala taron Brussels ba tare da cimma yarjejeniya ba

An sabunta: 24 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:56 GMT

Hedikwatar Tarayyar Turai a Brussles

Shugabannin Tarayyar Turai sun kammala taron su a Brussels ba tare da cimma yarjejeniya ba a kan sabon kasafin kudi.

Akasarin Shugabannin Tarayyar Turan sun amince ne a kan a yi kari a kasafin kudin na shekara ta dubu biyu da goma sha-hudu zuwa da ashirin, amma Birtaniya da Jamus da sauran wasu kasashen suna bukatar a zaftare yawan kasafin kudin.

Prime Ministan Birtaniya David Cameron ya ce akwai kudaden da ya kamata a zazzaftare, ya kuma ce ya yi imanin cewa za a iya cimma yarjejeniya akan batun.

Yace bai kamata Tarayyar Turan ta kara yawan kudin da take kashewa ba alhali a cikin kasashe ana zazzaftare kudaden da ake kashewa.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi karin haske a kan tattaunawar da suka yi, tana cewa ta yi imanin sun yi tattaunawa mai kyau.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.