BBC navigation

Mutane sama da 100 sun mutu a gobarar Bangladesh

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:15 GMT

Gobara a Bangladesh

Mutane fiye da dari daya sun rasa rayukan su a ranar Assabar a wata gobara da ta kurmushe wata masana'antar saka tufafi dake Dhaka babban birnin Bangladesh.

Ma'aikatan ceto sun gano gawarwakin mutane da dama a hawa daban-daban na ginin masana'antar wadda mallakar Tazreen Fashion ce.

Ma'aikatan da dama sun rasa rayukan su ne a yayinda suka yi kokarin dira ta tagogin ginin don tsere wa gobarar da ta tashi a cikin ginin Masana'antar.

Ma'aikatan kwana-kwana sun shafe kimanin sa'oi biyar kafin su kashe wutar a lardin Ashulia.

Har izuwa yanzu dai ba a tantance abinda ya haddasa tashin gobarar ba.

Shekaru biyu da suka wuce wata gobarar da aka yi a wata masana'antar saka tufafin a wannan lardin ta hallaka a kalla mutane ashirin da biyar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.