BBC navigation

Gobara ta hallaka mutane a wata masaka

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:45 GMT
Ginin masakar da gobara ta ci a Bangladesh

Ginin masakar da gobara ta ci a Bangladesh

Jami'ai a Bangladesh sun ce akalla ma'aikata 100 ne suka rasa rayukansu bayan da gobara ta tashi a wata masaka dake wajan babban birnin kasar Dhaka.

Ma'aikatan kashe gobara sun shaidawa BBC cewa sun gano karin wasu gawarwaki a baragusan ginin da safiyar yau dinnan.

Jami'ai sun ce wutar ta fara ne daga kasan dogon ginin masakar inda ake ajiye kayayyaki sannan nanan da nan ta bazu zuwa wasu bangarori na ginin.

Daruruwan ma'aikata ne gobarar ta ritsa da su.

Wani jami'in kashe gobara ya shaidawa BBC cewa da yawan ma'aikatan sun dirgo daga can kololuwar ginin dan tsera da lafiyarsu.

Zahurul Amin ya ce gaba daya sun samu gawarwakin mutane dari a hawa uku na ginin.

Ma'aikata da dama su ji raunuka kuma yawan mutanan da suka rasun na iya karuwa.

Ba'a dai kai ga gano abun da ya haddasa gobarar ba, amma dai jami'ai sun yi amannar cewa matsalar wutar lantarki ce ta janyota.

A kasar Banlgadesh dai ana yawan samun gobara ta sanadiyyar yadda ake hada woyoyin wutar lantarki a masana'antu abun kuma da ke jawo mutuwar ma'aikata da dama a kokace shekara a kasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.