BBC navigation

Shugabannin Gabashin Afrika na son kawo karshen rikici a Congo

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:25 GMT

Sojoji a Congo

Shugabannin yankin gabashin Afrika sun yi kira ga 'yan tawaye a gabashin Jamhuri'yyar Demokradiyyar Congo su kawo karshen hare-haren da suke kaiwa.

A wani taron Koli da suka yi a Kampala babban birnin Uganda, sun yi kira ga 'yan tawayen na kungiyar M23 su janye daga birnin Goma.

Shugabannin 'yan tawayen dai sun gana da Shugaban kasar Congo Joseph Kabila da nufin bude fagen shawarwari a yau Lahadi.

Shugabannin kasashen Afrikar hudu ne suka halarci taron kolin, amma banda Shugaban Rwanda, Paul Kagame.

Shugabannin kasashen yankin har ila yau sun yi shawarar tura wata rundunar sojoji ta hadin-gwiwa a filin jiragen sama na Goma tare da yin kira ga Mr Kabila ya share wa 'yan tawayen hawayen su.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.