BBC navigation

Muslim Brotherhood a Masar za su yi zanga-zanga

An sabunta: 25 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:20 GMT

Shugaban Kasar Masar Mohamed Mursi

Jam'iyyar Muslim Brotherhood ta yi kira a gudanar da zanga-zanga a yau Lahadi a duk fadin kasar Masar don nuna goyon baya ga Shugaba Mohammed Mursi.

Shawarar da Shugaban ya yanke ta baiwa kansa jerin sababbin iko; ta bakanta rayukan wasu 'yan kasar tare da nuna rarrabuwar kawuna tsakanin su.

Alkalai a kasar Masar sun dakatar da harkokin su a wani mataki na nuna rashin amincewa da shawarar ta Shugaba Morsi tare da yin kiran a sake nada babban mai gabatar da kara na kasar.

An nada alkalin ne tun zamanin mulkin Shugaba Mubarak wanda aka hambarar daga karagar mulki a bara.

Wani shahararren dan adawa Mohammed Al Baradei ya yi kira a cigaba da zanga-zangar lumana har sai Shugaban kasar ya canza shawara.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.