BBC navigation

Rahoton kotun manyan laifuka kan Boko Haram

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:10 GMT
Fatou Bensouda

An fidda rahota kan ƙungiyar Boko Haram

Babbar mai shigar da ƙara a kotun duniya Fatou Bensouda ta ce sun sami ƙwaƙƙwarar hujja da ke nuni da cewa 'ya'yan ƙungiyar Boko Haram sun aikata miyagun laifuka.

Rahotan ya yi bayani game da tashe-tashen hankulan da aka samu mai nasaba da addini da kuma ƙabilanci a jahohin Kano da Filato da Kaduna da kuma tarzomar data ɓarke a wasu jahohin ƙasar bayan bayyana sakamakon zaɓe

Sai dai rahotan yace babu wata ƙwaƙwarar hujja dake nuni da cewar an aikata miyagun laifuka a tashe tashen hankulan, kodayake rahotan yace zasu ƙara duba batun idan suka sami ƙarin shaidu game da shugabanni da kuma ƙungiyoyin da ake zargin su na da hannu a tashe tashen hankulan

Haka kuma babbar mai shigar da ƙarar tace babu wata ƙwaƙwarar hujja dake nuni da cewar ƙungiyar nan ta tsagerun Neja delta wato MEND ta aikata miyagun laifuka a tashe tashen hankulan da aka samu a yankin a shekarar 2009 , sai dai Fatou Bensouda tace zasu sake bincike idan su ka sami sabbin bayanai

Sai dai Fatou Bensouda tace sun sami ƙwaƙwarar hujjar dake nuni da cewar ƙungiyar Boko Haram ta aikata miyagun laifuka da su ka danganci take haƙƙoƙin bil adama tun daga shekarar 2009 zuwa yanzu

A cewar rahotan mutane fiye da 1,000 ne suka hallaka a hare haren da ƙungiyar ta kai a sassa daban daban na arewacin ƙasar

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.