BBC navigation

Gobara ta kashe mutane a masana'antar nakasassu a Jamus

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:10 GMT
Angela merkel

Gobara ta kashe mutane a jamus

Ma'aikatan kashe gobara a kudancin ƙasar Jamus sun ce mutane goma sha huɗu ne su ka mutu, a wata gobara da ta tashi a wata masana'anta ta nakasassu.

Wasu mutanen aƙalla shida kuma sun ji rauni sakamakon wannan wuta da ta tashi a garin Titisee-Neustadt.

Ma'aikatan ceto sanye da na'urar shaƙar iska sun kutsa kai cikin bakin hayaƙin da ya turnuƙe, domin ceto wasu daga cikin waɗanda gobarar ta rutsa da su

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.