BBC navigation

Jamiyyar CIU ta yi nasara a zaben Spain

An sabunta: 26 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:33 GMT

Artur Mas na CIU

Jam'iyyar dake goyon bayan samun 'yancin yankin Catalonia na kasar Spain sun ci zaben Majalisau da gagarumin rinjaye a kasar.

Bayan da aka kidaya kusan dukan kuri'un, Jam'iyyar CIU wadda ta yi alkawarin shirya kuri'ar raba gardama game da 'yancin kan, ita ce ta cinye kujeru hamsin - watau kiris ya rage ta cinye mafi rinjayen kujerun.

Wata Jam'iyyar ta 'yan kishin kasa Republican Left, ta samu kujeru ashirin da daya, ta zo matsayi na biyu a zaben.

Shugaban jam'iyyar CIU Artur Mas, ya shaidawa BBC cewar zai nemi ra'ayin jama'a a game da 'yancin kan yankin na Catalonia a cikin wasu shekaru hudu masu zuwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.