BBC navigation

An hako gawar Yasser Arafat

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 12:04 GMT

Marigayi Yessar Arafat

An hako gawar tsohon jagoran Falasdinawa Yasser Arafat a wani bangare na binciken da ake yi kan musabbabin mutuwarsa.

An baiwa masana daga Switzerland, Faransa da Rasha gwaje-gwajen da aka yi masa domin su tantance abinda yayi ajalin marigayin a wani asibiti a birnin Paris na Faransa a shekara ta 2004.

Tuni dai aka sake binne Mr Arafat, sannan aka rufe wurin da kushewar ta sa take.

Zargin da ake yi shi ne na cewa an kashe Arafat ne mai shekaru 75, ta hanyar sanya masa guba.

Kasar Faransa ta fara gudanar da bincike kan cewa an kashe shi ne a watan Agusta, bayan da wasu masana daga Switzerland suka gano sanadarin radioactive polonium-210 a kayansa.

Bayanan lafiyarsa dai sun nuna cewa ya yi fama da cutar bangaren jiki ne.

Uwargidansa Suha, ta ki amince wa a gudanar da gwaji a lokacin da ya rasu, sai dai ta nemi hukumomin Falasdinu su bayar da izinin hako gawar "domin tantance ainahin abinda ya faru".

Sake tono gawar Mr Arafat daga kabarinsa da ke Gabar yammacin Kogin Jordan ya biyo bayan wani shiri ne na talabijin na Aljazeera ya watsa; wanda ya yi zargin cewar an gano wasu 'yan alamomi na wata guba a tufafin na Mr Arafat.

Falasdinawa da dama dai sun yi zargin Isra'ila na da hannu a mutuwar Mr Arafat, zargin da a kowanne lokaci Isra'ilar ke musantawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.