BBC navigation

Faransa za ta goyi bayan Falasdinawa

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:50 GMT
Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da Ban ki Moon

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon

Kasar Faransa ta bayar da tabbacin cewa za ta goyi bayan yunkurin Falasdinawa na samun wakilci a matsayin kasa 'yar kallo a Majalisar Dinkin Duniya.

Ministan harkokin waje Laurent Fabius ya ce Faransa ta dade tana goyon bayan yunkurin Falasdinawa na samun cikakkiyar kasa, kuma za ta kada kuri'ar goyon bayan haka.

Falasdinawa na neman babban taron Majalisar ne ya amince da bukatarsu na zamowa 'kasa 'yar kallo' a Majalisar maimakon matsayinta na yanzu na 'yar kallo amma ba kasa ba.

Nan gaba a wannan makon ne za a kada kuri'a kan wannan batu.

"Ranar Alhamis ko Juma'a, idan aka nemi a kada kuri'a, Faransa za ta goyi bayan yunkurin Falasdinu," kamar yadda Mr Fabius ya shaida wa Majalisar dokokin Faransa.

Faransa - wacce keda kujerar naki a Majalisar - ita ce babbar kasar Turai ta farko da ta fito ta nuna goyon baya ga yunkurin na Falasdinawa.

Isra'ila ta yi gargadin cewa idan wannan shiri ya samu amincewa, to za a sabawa yarjejeniyar Oslo ta 1993, wacce ta kafa hukumar Falasdinawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.