BBC navigation

'Yan takara a Ghana sun cimma wata yarjejeniya

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:03 GMT
Shugaba John Dramani Mahama na Ghana

Shugaba John Dramani Mahama na Ghana na shan layar kama aiki

'Yan takarar Shugabancin kasar Ghana na sun kulla wata yarjejeniya a birnin Kumasi dake jihar Ashanti a gaban babban sarkin Daular Ashanti, Asantehene Otumfuor Osei Tutu II don tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben mai zuwa.

An dai bukaci 'yan takarar shugabancin da su kulla yarjejeniyar ce sakamakon tashe tashen hankulan da ake ci gaba da samu a sassa daban- daban na kasar musamman tsakanin magoya bayan manyan jami'yyun siyasar kasar na NDC mai mulki da kuma babbar jami'yyar adawa ta NPP.

A ranar 7 ga watan Disamba ne dai za a yi zaben kasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.