BBC navigation

Ministoci a Turai sun amince a rage bashin Girka

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:14 GMT

Girka

Ministocin harkokin kudi na Tarayyar Turai sun cimma yarjejeniya a kan batun rage bashin dake kan kasar Girka tare da share wa kasar hanyar samun tallafin da ta dade tana jira na bashin da zai farfado da tattalin arzikinta.

A shawarwarin da suka kai tsakiyar dare suna yi a Brussels, Ministocin sun amince Asusun ba da tallafi na IMF ya baiwa kasar ta Girka bashin fiye da dola billiyan hamsin tun daga Disamba - a karkashin wasu sharudda.

Tun cikin watan Yuni kasar Girka ke jiran kudin, don su taimaka mata ta farfado da tattalin arzikinta da bashi ya dabaibaye.

Shugabar Asusun ba da lamuni ta duniya IMF Christine Lagarde ta ce an sha fama a tattaunawar to amma ta yi amfani.

Tace kasar ta Girka da takwarorin ta na Tarayyar Turai sun yi abinda ake bukata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.