BBC navigation

'Yan adawa a Masar za su yi zanga-zanga

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:35 GMT

Zanga-zanga a Masar

Kungiyoyin 'yan adawa a kasar masar suna shirin wata gagarumar zanga-zanga don nuna rashin amincewa da Shugaba Mursi wanda a makon da ya gabata ya baiwa kan sa jerin sababbin iko.

Shugaban kasar ya yi kokarin yayyafa ruwa ga wutar rikicin inda ya yi jawabi cewa kariyar da ya baiwa kansa daga tuhuma na nufin bayar da kariya ne ga hukumomin kasa, kuma matakin ba zai kare dukkan shawarwarin da ya zartas ba.

Duk da jawaban Shugaban, 'yan adawa suna bukatar Shugaban kasar ya janye baki-dayan shawarwarin, suna cewa sun saba wa demokradiyya.

Jam'iyyar Muslim Brotherhood ta soke gangamin da ta shirya yi don nuna goyon baya ga Shugaban kasar don gudun arangama tsakanin su da 'yan adawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.