BBC navigation

Yunkurin hadin kai tsakanin ANC da PDP

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:15 GMT

PDP

Jam'iyyar PDP ce ke rike da madafun iko a Najeriya tun 1999

Jam'iyyar ANC mai mulkin kasar Afirka ta kudu na ziyara ga takwararta ta PDP mai mulkin Najeriya da nufin karfafa kawance tsakanin junansu.

Jam'iyyun biyu da ke ikirarin cewa su ne manya a nahiyar Afirka sun bayyana cewa akwai bukatar su hada kai da juna ta yadda nahiyar za ta ci gaba.

Da jam'iyyar ANC ta kasar Afirka ta kudu da kuma jam'iyyar PDP mai mulkin Najeriya duka sun ce ba wannan ne karon farko da suke mu'amala da juna ba, saboda haka manufar ziyarar ba ta wuce yaukaka dankon zumunci tsakanin su ya su ba.

"Kalubalen da muke fuskanta a nahiyar Afirka na bukatar hadin kai wajen tunkararsa. Saboda haka jam'iyyar ANC da PDP na bukatar tafiya tare. Kuma abin da muka zo karfafawa kenan," a cewar jagoran tawagar ANC Mathew Phosa.

'Kawance ne mai muhimmanci'

Ya kara da cewa akwai bukatar su hada hankali wuri guda ta yadda za su daidaita alkiblar nahiyar Afirka a kan tafarkin habaka da bunkasa a matakai daban-daban.

"Muhimman al'amura da ke faruwa a duniya na bukatar mu hada kai a siyasance don ba wa juna shawara a matakin kungiyar tarayyar Afirka ko Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin da ake da su a nahiyar Afirka da duniya baki daya".

ANC

ANC na fuskantar kalubale a Afrika ta Kudu inda za a yi zaben shugaban kasa kwanan nan

"Wannan kawance ne mai muhimmanci a tsakaninmu, akwai abinda za mu koya daga wurinsu, suma kuma akwai abinda za su koya daga wurinmu," kamar yadda shugaban PDP Alhaji Bamanga Tukur ya shaida wa BBC.

Da jam'iyyar ANC da kuma PDP kowace na jin cewa ta zarce sa'a a Nahiyar Afirka, saboda ANC na alfahari da karfin akida da yawan shekaru, kasancewar ta shafe tsawon karni guda da kafuwa.

Yayin da jam'iyyar PDP ke tinkaho da yawa, kasancewar ita ke mulkin kasar ta fi yawan jama'a a nahiyar, saboda kiyasi na nuna cewa al'umar Najeriya ta kai sama da miliyon dari da sittin.

Bakin jam'iyyu biyun dai ya zo daya cewar akwai bukatar masu mulki a nahiyar Afirka su mai da hankali wajen samar da ilimi ga jama'arsu, tare da habaka tattalin arzikin kasashen nahiyar ta hanyar bunkasa noma ta yadda mafi yawan al'umominsu kasancewarsu manoma za su ji ana damawa da su.

Ayarin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar Afrika ta kudun ya kai caffa ga shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan, inda suka yi wata ganawa ta sirri.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.