BBC navigation

An soma wayar da kan jama'a kan amfani da iskar gas a Nijar

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:35 GMT
Nijar

Nijar na bukatar al'umma su soma amfani da iskar gas wajen girki

A jamhuriyar Nijar Ma'aikatar ministan makamashi da man fetur ta ƙaddamar da wani shiri dake da burin mayar da hankalin 'yan ƙasar wajen amfani da iskar gas domin yin girki maimakon dogaro da ice.

Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kuka da gurgusowar hamada a cikin ƙasar ta Nijar .

Shirin dai ya tanadi sayarwa jama'a da iskar gas ɗin ta girki a cikin farashi mai rahusa.

Ministan makamashi da man fetur , Fumakoi Gado ya faɗawa BBC cewa gas ɗin da Nijar ke da shi yafi na duk ƙasashen Afirka arha, a saboda ya ce za a rinƙa sayarwa da ‘yan ƙasar a farashi mai rahusa

Ma’aikatar makamashin da man fetur ta soma wannan gangami na wayar wa da mutane kai a birnin Yamai, daga nan kuma zata rankaya zuwa wasu garuruwan ƙasar domin tabbatar da mutane sun koma amfani da iskar ta gas wajen girki

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.