BBC navigation

Za a tono gawar Yessar Arafat

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:27 GMT

Marigayi Yessar Arafat

Nan gaba kadan ne a yau Talata kwararru za su tono gawar tsohon Jagoran Palasdinawa Yessar Arafat a kokarin nazarin ko gaskiya ne an dura masa guba ne ya mutu ko kuma akasin haka.

Mr Arafat ya mutu ne a shekara ta dubu biyu da hudu a Faransa bayan wata gajeruwar rashin lafiyar da ba a tantance ta ba.

Tono shi da za a yi daga kabarinsa dake Gabar yammacin Kogin Jordan ya biyo bayan wani shiri ne na talabijin da aka watsa; wanda ya yi zargin cewar an gano wasu 'yan alamomi na wata guba a tufafin na Mr Arafat.

Palasdinawa da dama dai sun yi zargin Isra'ila na da hannu a mutuwar Mr Arafat, zargin da a kowanne lokaci Isra'ilar ke musantawa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.