BBC navigation

An kashe mutane goma a Filaton Najeriya

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:37 GMT
Jami'an tsaro a Nijeriya

Jami'an tsaro a Nijeriya

Hukumomin tsaro a Jihar Filaton Nijeriya sun tarwatsa wasu mutane da suka fito kan titi domin nuna rashin jin dadinsu, dangane da wani harin da aka kai ranar Litinin da daddare a wata mashaya a garin Heipang, inda mutane goma suka mutu.

Rahotanni sun kuma ce wasu karin mutanen da dama sun samu raunuka.

Wasu da suka shaida lamarin sun ce wadanda suka kai harin sun je ne a motar soja, sanye da kayan sarki na soja, inda suka bude wutairin na kan-maitsautsayi.

To sai dai kuma rundunar tsaro dake aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato ta musanta zargin hannun jami'anta a kashe-kashen, tana mai cewa tana gudanar da bincike kan lamarin.

Jihar Filaton dai ta yi kaurin suna wajen tashe-tashen hankula masu nasaba da addini da kuma kabilanci, lamarin da ya haddasa asara ta rayuka da kuma dukiya mai dimbin yawa a shekarun da suka wuce.

A karo da dama, bangarorin Musulmi da na Kirista da ake samun takun-saka tsakaninsua jihar ta Filato kan yi korafin cewa jami'an tsaro na da hannu wajen kai masu hare-hare, zargin da a kodayaushe jami'an tsaron kan fito su musanta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.