BBC navigation

'Yan tawaye a Syria sun kame wani yanki

An sabunta: 27 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:40 GMT

Aman wuta a Syria

'Yan tawaye a kasar Syria sun ce sun kame wata madatsar ruwa dake kogin Euphrates a yankin arewacin kasar.

Wani wakilin BBC ya ce idan har hakan ta tabbata, kwace madatsar ruwan ta Tishrin za ta kara baiwa 'yan tawayen damar cin dunun Aleppo babban birnin kasuwancin Syria.

Dama kusan rabin birnin yana hannun 'yan tawayen.

'Yan adawa masu fafutuka sun ce wani jirgin yaki na gwamnati ya jefa bam a kan wani Kauye dake hannun 'yan tawayen a kusa da Damascus babban birnin kasar inda Yara goma suka mutu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.