BBC navigation

'Assange na fama da matsanancin ciwon huhu'

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:05 GMT

Julian Assange mai shafin kwarmata bayanai na Wikkileaks

Jakadiyar kasar Equador a Birtaniya ta ce wanda ya kirkiro shafin nan mai kwarmata bayanai na Wikkileaks, Julian Assange na fama da rashin Lafiya.

Ana Alban Mora ta ce Mista Assange yana fama ne da matsananciyar cutar huhu kuma zai iya kara shiga cikin mawuyacin hali a kowane lokaci.

Julian Assange dai ya samu mafaka a ofishin jakadancin Equador dake London tun watanni biyar da suka wuce domin kaucewa kama shi da kuma tasa keyarsa zuwa kasar Sweden inda za a yi masa tambayoyi kan zarge-zargen aikata fyade.

Tun a watan jiya ne dai Kasar Equador ta baiyyana damuwa game da halin lafiyar Mr. Julian Assange, inda har ta roki Birtaniya da ta ba shi damar fita zuwa asibiti idan bukatar hakan ta taso.

Gwamnatin Birtaniyar ta ki amsa rokon, inda ta ce za a kama shi da zarar ya tako kafarsa wajen ofishin jakadancin.

Ganawa da Hague

Sai dai Jakadiyar ta ce idan ba a bar shi ya fita ba, to halin da ya ke ciki zai iya kara muni.

''Mr. Assange kamar yadda kowa ya sani yana killace ne a dan karamin wuri. Ko baya ga cewar ofishin jakadancin mu yana da tagogi kalilan ne, shima birnin London kansa ba bu isasshen haske a wannan lokaci na shekara. Don haka yana iya samun kowane irin lahani sakamakon rashin hasken rana da kuma rashin tsaftattacen iskan shaka.'' Inji Miss Alban Mora.

Inda ta kara da cewar tana sa ran zata gana da Sakataren harkokin wajen Birtaniyar , William Hague da kuma Sakatariyar harkokin cikin gida Tharesa May domin tattaunawa kan makomar Mr. Assange.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.