BBC navigation

Ana dakon rahoton Leveson a Birtaniya

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:08 GMT

Mai shara'a Leveson wanda ya gudanarda bincike

A Birtaniya, ’yan jarida ne za su zama kanun labarai in an jima can, yayin da wani alkali, Mai shari’a Leveson zai fayyace sakamakon binciken da ya gudanar, game da batun satar sauraren zantuttukan da akan yi ta waya.

Ana sa ran rahoton zai kwatanta yadda satar sauraren wayar take da kuma sauran wasu haramtattun abubuwa da ake yi kamar yadda suka zama ruwan dare.

Kana ya yi suka game da dangantakar da ake kullawa a tsakanin masu kafofin yada labarai da ’yan siyasa.

Mai yiwuwa kuma rahoton ya bayar da wasu tsauraran shawarwari, wadanda za su saka kaidi kan al’amuran kafofin yada labarai a cikin shekaru fiye da dari uku.

Jawabi a majalisa

Ana sa ran Firay Ministan Birtaniya David Cameron ya bayyana abin da yake nufin yi da sakamakon bincike a gaban majalisar dokoki inda an jima.

An dai samu kamun kafa mai tsanani daga bangarorin da ke goyon baya da kuma masu adawa da baiwa 'yan jaridu cikakken 'yanci, yayin da bincike ke gudana.

An dai soma binciken ne bayan da ta bayyana cewa jaridar News of the world ta saci bayanan wayar Milly Dowler, wata yar makarantar da aka kashe a shekera ta dubu biyu da biyu.

Wannan dai ya kai 'Yan majalisar Burtaniya yiwa wanda ya mallaki jaridar tambayoyi a watan yulin 2011 dangane da watsin da jaridarsa ta yi da dokokin yada labarai, wadanda suka hana yin kutse ga sirrin jama'a.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.