BBC navigation

Ana cece kuce kan shirin rusa gidaje a Jos

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:57 GMT

Wasu gidajen da suka rushe sakamakon ambaliyar ruwa a Jos

A Jihar Filaton Nijeriya ana takaddama tsakanin gwamnati da mazauna wasu gidaje dake kusa da fadar Gbong Gwom Jos, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar, dangane da shirin gwamnatin na rusa gidajen da sauran kadarorinsu.

Gwamnatin dai ta bayyana cewa daukar matakin ya zamo wajibi domin samar da sarari ga Gbong Gwom din wanda a halin yanzu ba ya zama a cikin fadar tasa dake tsakiyar unguwar da musulmi suka fi rinjaye a birnin dake yawan fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da kuma addini.

Sai dai kuma masu gidajen na adawa da matakin, saboda a cewar su wani yunkuri ne na raba su da muhallansu domin wata boyayyiyar manufa.

Da dama daga cikin mazauna gidaje kimanin arba’in da gwamnatin jihar Filaton ke cewa za ta rusa a kewayen fadar sun ce ba za su sayar da gidajen ba kuma ba su da niyyar tashi daga matsugunansu na iyaye da kakanni.

Wasu masu gidajen sun ce gidajen na su sun riga Fadar basaraken gargajiyar kafuwa a wurin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.