BBC navigation

An kashe Uba da 'ya'yansa biyu a Karu

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:18 GMT
Wasu jami'an tsaron Nijeriya

Wasu jami'an tsaron Nijeriya

A jihar Nasarawan Nijeriya ana tayar da jijiyoyin wuya dangane da kisan wasu Fulani makiyaya 'yan gida daya, su uku da ake zargin 'yan-sanda da aikatawa.

Lamarin dai ya faru ne jiya a garin Nike dake karamar hukumar Karu, bayan wata takaddama tsakanin makiyayan da wani manomi wanda ya zargi wani makiyayi da barin dabbobinsa suka yi masa barna a gona.

A sakamakon haka ne aka ce manomin ya kai kara wajen 'yan sanda domin su sasanta su.

To sai dai kuma rahotanni na cewa 'yan sandan da suka je sasantawa bisa gayyatar manomin, sai suka bindige Fulanin uku, da suka hada da uba, da 'ya'yansa biyu magidanta, a cikin gidansu.

Hukumomin 'yan sanda a jihar ta Nasarawa sun ce suna gudanar da bincike kan batun.

Kisan na Karu na zuwa ne, kwana guda bayan kashe wasu mutane kimanin goma a Heipang jihar Pilato, bayan da aka yi zargin wasu mutane cikin kayan soja siun bude masu wuta a wata mashaya.

Ko a kwanakin baya dai wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a sun zargi jami'an tsaro a Nijeriya da aikata kisan gilla ba tare da shari'a ba, zargin da jami'an tasron kan fito su karyata.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.