BBC navigation

Rice ta amsa boye gaskiya kan harin Bengazi

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 10:05 GMT

Jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin duniya Suzan Rice

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Suzan Rice ta amsa cewa wani bangare na bayanin da ta bayar game da harin da aka kaiwa ofishin jakadancin Amurka a Bengazi ba dai-dai ba ne.

A lokacin da mutuwar Jakadan Amurka da wasu Jami'ansa uku a Bengazin, Susan Rice ta ce lamarin ya faru ne sakamakon wata zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma, amma daga bisani bayanan asiri suka musanta hakan da cewa an tsara kai harin ne tun kafin tarzomar.

Ms. Rice dai ta amsa cewa kalamanta na farko ba dai-dai ba ne, amma kuma ta musanta cewa ta yi kokarin sa Amurka yarda da abin da ba gaskiya ba ne.

Tana dai kokarin shawo kan 'yan jam'iyyar Republican ne wadanda suka ce za su hana nada ta sakatariyar harkokin wajen kasar da shugaba Obama ke son yi a wa'adin mulkinsa na biyu.

Ganawar sirri

Jakadiyar dai ta yi wata ganawar sirri ta kusan awa daya a jiya da Senatocin Jam'iyyar ta Republican ukku wadanda ke barazanar kada kuri'ar rashin amincewa da nadinta.

Amma Senatocin ukku watau Sen. John Mccain, da Lindsey Graham da kuma Kelly Ayotte sun ce sun ma kara samun damuwa bayan ganawa da ita; kuma suka ce gwamnatin Obama tayi kokarin rufe bangaren da ke nuna cewar harin ta'addanci ne domin kaucewa karyata da'awar da Shugaban Kasar yayi ta samun nasara kan kungiyar Alka'ida gabanin zaben shugaban kasa na shida ga watan Nuwamba.

Ana dai saran Ms. Rice ce za a bayar da sunanta domin ta maye gubin Hillary Clinton a zaman sakatariyar Harkokin waje kasar wadda za ta ajiye aike a shekara mai zuwa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.