BBC navigation

Wasu abubuwa sun fashe a Jarmana na Syria

An sabunta: 28 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 10:01 GMT
Wasu abubuwa sun fashe a garin garin Jarmana

Barnar da fashewar wasu abubuwa suka janyo a garin Jarmana

Kamfanin dillancin labarai na Syria, SANA ya bada rahoton fashewar wasu abubuwa guda biyu a garin Jarmana dake da nisan kilomita goma da birnin Damuscus.

Rahotannin sun ce 'yan ta'adda ne ke da alhakin fashewar abubuwan da suka yi sandiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

Wata kungiyar 'yan adawa ta kasar ta ce an dana bama-baman ne a cikin wasu motoci guda biyu.

Mai aiko wa BBC rahotanni a garin na Jarmana ya ce tun da fari an yi artabu tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a yau Laraba.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.