BBC navigation

An tono gawarwakin mutane a kasar Benin

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:26 GMT
Shugaba Boni Yayi na Benin

Shugaba Boni Yayi na Benin

'Yan sanda jamhuriyar Benin sun ce an lalata kaburbura kimanin dari a wata makabarta kusa da Porto Novo, babban birnin kasar.

Sun ce an yanke kawunan gawarwakin da aka tono daga kaburburan, an kuma cire wasu aga cikin sassan jikinsu.

Wakilin BBC a jamhuriyar Benin bisa dukkan alamu wasu dake so su sayar da sassan jikin ne wajen hada magungunan samun sa'a suka cira domin sayarwa.

Ya ce mai yuwa za a yi amfani da su ne wajen tsafe tsafe da tsibbace tsibbace wadanda suka zama ruwan dare a jamhuriyar ta |Benin.

Irin wannan matsala ta tona kaburbura domin cirar sassan jikin gawa bai tsaya a kasar ta Benin ba, a galibin kasashen Afrika ana yin irin wannan dabi'a wadda wasu ke dangantawa da talauci da kuma rashin ilmi.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.