BBC navigation

An soki yadda jaridun Burtaniya ke aiki

An sabunta: 29 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:31 GMT

Mai shara'a Leveson wanda ya gudanar da bincike

Akwai bukatar samar da dokar "saka wa kai dokoki ga jaridun Burtaniya" domin inganta aikin jarida a kasar, a cewar rahoton mai shari'a Leveson.

Kwamitin da ya gudanar da bincike game da daidaitattun ka'idojin aikin jarida a Burtaniya ya soki wasu Jaridu da rashin kimtsi da kuma yin aiki ta wasu hanyoyin da ba su dace ba.

An dai jima ana jiran rahoton a Burtaniya kan batun satar saurare da shiga shafukan sakonnin wayar salula da kuma ka'idojin aikin Jarida.

Mai shari'a Leveson ya ce "jaridun sun jefa rayuwar mutanen da basu-ji-basu-gani ba cikin mawuyacin hali a shekaru da dama".

Ya ce shawarar da ya bayar za ta taimaka wurin kare hakkin wadanda aka take wa hakki da kuma wadanda ke kai korafi.

Ya kuma soki dangantaka tsakanin 'yan siyasa da 'yan jarida a shekaru ashirin din da suka gabata, wacce yace "ta yi muni".

Jawabi a majalisa

Fira minista David Cameron ne ya kafa kwamitin binciken a watan Yulin bara bayan da ta tabbata cewa 'yan jaridar News of the World sun saci bayanan wata yarinya 'yar makaranta da aka kashe Milly Dowler.

Kamfanin News International da ya mallaki jaridar dai ya rufeta sakamakon badakalar.

Kwamitin ya saurari bahasi daga 'yan siyasa da 'yan jarida da kuma wadanda kafafen yada labarai suka yiwa ba daidai ba.

Ana sa ran Firay Ministan Birtaniya David Cameron ya bayyana abin da yake nufin yi da sakamakon bincike a gaban majalisar dokoki inda an jima.

An dai samu kamun kafa mai tsanani daga bangarorin da ke goyon baya da kuma masu adawa da baiwa 'yan jaridu cikakken 'yanci, yayin da bincike ke gudana.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.