BBC navigation

Isra’ila za ta gina sabbin gidaje 3,000 a yankin Palasɗinawa

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:31 GMT
Mahmoud Abbas

Isra'ila zata gina gidaje a filayen Palasdinawa

Isra’ila ta bada umarnin gina sabbin gidaje 3,000 a filayen Palasɗinawa da take mamaye da su.

Wannan mataki dai na zuwa ne kwana guda bayan da majalisar ɗinkin duniya ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da Palasɗinu a matsayin ƙasa 'yar kallo marar wakilci

Wani wakilin BBC yace a fili take cewa Israila tana jin barin wannan cigaba da aka samu ya wuce ba tare da ta maida wani martani na siyasa ba, zai sa a ai mata kallo na rauni

Hukumomin Palasɗinawa dai sun ce ba zasu dawo tattanawar zaman lafiya ba har sai Isra’ilan ta dakatar da gine ginen

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.