BBC navigation

Falasɗinawa sun yi shagulgulan samun amincewar majalisar ɗinkin duniya

An sabunta: 30 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:24 GMT

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya mike tsaye yana tafi bayan fitarda sakamakon kuri'ar.

An yi ta bukukuwa a gaɓar yammacin kogin Jordan da kuma zirin Gaza bayan da majalisar ɗinkin duniya ta kaɗa kuri'ar ɗaukaka matsayin Palasɗinawa.

Zauren majalisar ɗinkin duniyar dai da gagarumin rinjaye ya bada goyon baya game da matakin baiwa Palasdinawa matsayin kasa 'yar kallo marar wakilci.

Shugaba Mahmoud Abbas ya ce wani lokaci ne mai cike da tarihi, amma sai dai mai magana da yawun gwamnatin Isra’ila Mark Regev ya yi watsi da wannan al'amari, yana mai cewa matakin zai yi illa ga koƙarin samar da zaman lafiya.

Wakilan Ƙasashe 138 ne suka jefa kui'ar goyon baya daga cikin na Ƙasashe 193 dake zauren,yayinda 9 suka nuna adawa, 41 kuma suka ki ɗaukar kowane ɓangare.

Isra'ila da Amurka dai, na cikin kasashe tara da suka kaɗa kuri'ar ƙin amincewa da wannan matsayi da Palasɗinawa suka samu.

Kuri'ar ta Majalisar Dinkin Duniya a kaikaice ta amince ne da kafuwar Ƙasar Falasdinu tare da ba ta damar zama wakiliyar a hukumomi kamar su Kotun Hukumta Manyan Laifukka ta Duniya (ICC).

Isra'ila tare da Amurka na fargabar hakan zai kai Falasdinawa shigar da kara kanta bisa aikata laifukan yaƙi ko kuma fadaɗa matsugunan yahudawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Martani

Farayin Ministan Isra'ila Benyamin Natanyahu ya kira kuri'ar 'maras ma'ana' kuma yanzu masu lura da al'amurra za su sanya ido su ga irin martanin da ƙasar sa za ta mayar a hukumance.

Sai dai martanin da jama'a suka mayar a gabar yammacin kogin jordan mai kayatarwa ne.

Mutane sun yi cincirindo a Ramallah suna shawagi da tutoci, suna harba bindigogi a sama, suna kuma kabbara.

Falasɗinawan dai sun yi imanin cewar samun matsayin ƙasa 'yar kallo a Majalisar Ɗinkin Duniya zai kai su ga mataki na gaba a kokarin samun ƙasar su ta kansu, kuma ya kawo ƙarshen faɗansu da Isra'ila.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.