EU ta amince da shirin ceton bankuna

Shugabannin tarayyar Turai
Image caption Shugabannin tarayyar Turai

Ministocin kudi na kungiyar Tarayyar Turai da ke yin wani taro a Brussels sun amince su saki fiye da dala biliyan 60 ga kasar Girka a rukunin baya bayan nan na bashin kasashen duniyar da take ci.

Za a biya kusan dala biliyan 45 a cikin kwanaki masu zuwa.

Za a bayar da kudin ne a madadin zabtare kudaden da gwamnatin kasar Girka take kashewa da kuma wata yarjejeniyar da ta cimma tare da masu saka jari masu zaman kansu wadda a cikinta gwamnatin Girka za ta sake sayen wasu daga cikin takardun bashinta a wani farashin da aka rage domin rage nauyin bashin dake kanta.

Tun farko ministocin sun amince da wani shiri na sa babban bankin Turai ya kasance shi kadai ne mai sa ido kan galibin bankuna -- wani mataki mai muhimmanci ga warware matsalar bashin da ke shafar kasashe masu amfani kudin Euro.