Jama'iyar NPP a Ghana na duba halin zuwa kotu

Nana Akufo-Addo
Image caption Nana Akufo-Addo

Babbar Jama'iyar adawa ta NPP a Ghana ta ce tana duba yiwuwar kalubalantar sakamakon zaben Shugaban kasa a kotu bayan da ta samu wata halayyar zargin magudi a nasarar da Shugaba mai ci John Dramani Mahama ya samu.

Shugaban Jama'iyar Jake Obetsebi -Lamptey ya shedawa manema labarai bayan wani taron jama'an jama'iyar,ciki har da dantakararta Nana Akufo-Addo, wanda bai ce uffan ba, amma ana sa ran zai yi magana daga bisani, cewar suna jinjina damar garzayawa zuwa kotu.

Shawarar ta zo ne yayinda kasar take cikin matsi na tabbatar da kimarta a matsayin wata kasa mai tsarin demokuradiya dake aiki a yankin yammacin Afrika mai fama da rikici.

Kamar yadda hukumar zabe ta ce Mahama ya lashe zaben ne da aka yi ranakun Juma'a da Asabar da fiye da kashi hamsin cikin dari , idan aka kwatanta da kashi fiye da arba'in da bakwai da Akufo -Addo ya samu.

Karin bayani