An yi zanga zangar hamayya a Masar

Masu zanga zanga a Masar
Image caption Masu zanga zanga a Masar

Dubun dubatar mutane sun kwarara kan titunan Alkahira babban birnin Masar domin wata zanga zangar hamayya da juna gabanin kuri'ar raba gardamar da za a yi ranar asabar.

Masu zanga zangar kin jinin Gwamnati sun keta shingayen da ke kare fadar Shugaban kasa.

Suna dai neman Shugaba Mohammed Morsi, ya soke kuri'ar raba gardamar a kan wani sabon tsarin mulki, magoya bayansa kuma suna cewar ya kamata a ci gaba da gudanar da ita.

Wani wakilin BBC dake wajen ginin yace daruruwan masu zanga zanga sun shige kariyar da aka sanya, kuma sojoji ba su dauki wani mataki a kansu ba.

Babban hafsan Soji na kasar ya bukaci dukanin bangarorin al'umar Masar da su hadu a wata sansantawa ta kasa afilin wasa na Olympic a Alkahira domin yin tattaunawa a gobe.

Karin bayani