Mutanen Na-Rabi a Jihar Bauchi sun yi zanga zanga

Taswirar Najeriya mai nuni da Jihar Pilato
Image caption Taswirar Najeriya mai nuni da Jihar Pilato

Mutanen garin Na-Rabi a karamar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, wanda ke kan iyakar jihohin Bauchi da Filato , sun yi wata zanga-zangar lumana.

Sun yi zanga zangar ne domin nuna rashin jin dadinsu kan wani wurin binciken ababen hawa na jamiā€™an tsaro dake garin.

Sun yi korafin cewa wurin binciken ababen hawar na haddasa munanan haduran mota da kan yi sanadiyar asarar rayukan mutane da dukiya mai yawa.

Wurin binciken ababen hawan dai na daidai wata gangara ce inda manyan motocin dakon kaya da tankokin mai suka sha ruftawa cikin jerin motoci da kuma kan duk wani mai tsautsayi dake kusa.

Koda a makon da ya gabata ma an samu irin wadannan hadura inda wata tankar mai ta afka wa kananan motoci kana ta kashe mutane ciki hard a wani soja dake wurin binciken ababan hawan.

A yau ma dai an samu wani hadarin a wannan wurin binciken ababen hawan.