Senegal za ta kafa kotun yiwa Hissene Habre shara'a

Hissene Habre, tsohon Shugaban Chadi
Image caption Hissene Habre, tsohon Shugaban Chadi

Majalisar dokokin kasar Senegal ta amince da wata doka da aka dade ana jira, ta kafa wata kotun musamman wadda za ta yi shari'a ga tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre.

Tun 2005 ake masa daurin talala ne a kasar ta Senegal, inda ya tsere bayan kifar da gwamnatinsa.

Shi dai yana musanta zargin da ake masa na kisan kai, da azabtar da dubban mutane, lokacin mulkinsa daga 1982 zuwa da casa'in.

Dokar ta bayar da umurnin kirkirar wasu kotunan Afrika na musamman a karkashin tsarin shara'a na Senegal.

A halin yanzu kungiyar tarayyar Afrika za ta nada alkalan kasar ta Senegal da wani wanda ba dan kasar Senegal din ne ba, amma kuma alkali ne dan Afrika domin yin shara'ar.