Park Guen-Hye ta lashe zabe a Koriya ta Kudu

Park Guen-Hye, sabuwar zababbiyar Shugabar Koriya ta Kudu
Image caption Park Guen-Hye, sabuwar zababbiyar Shugabar Koriya ta Kudu

Kasar Koriya ta kudu ta zabi mace a karon farko a matsayin shugabar kasa.

Ita ce kuma 'yar takarar jam'iyyar masu ra'ayin rikau, Park Guen-hye, wadda mahaifinta yayi mulkin sojin kasar shekaru 18 da suka wuce.

Wanda ya yi takara da Ms Park's Moon Jae-in, ya amince da kayen da aka yi masa.

Park Geun-hye ta yi alkawarin ganin cewa ta daidaita al'umura a kasar inda kowa zai iya amfana da daga albarkatun kasar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Banki Moon wanda tsohon ministan kasashen waje ne a kasar ya taya kasar murnar gudanar da zabe.

Ya ce; "Jamhuriyar Koriya da mutanenta sun nuna dattaku a harkokin siyasarsu, musamman yadda suka gudanar da zabe cikin lumana."

Sai dai nasarar da Park Geun-hye ta samu na nuni da cewa 'ya'yan tsaffin shugabanin soji ne za su jagoranci kasar koriya ta arewa da ta kudu.