Amurka za ta tura makaman Patriots zuwa Turkiya

Leon Panetta, Sakataren harkokin tsaron Amurka
Image caption Leon Panetta, Sakataren harkokin tsaron Amurka

Sakataren tsaron Amurka, Leon Panetta ya sanya hannu kan wani umurni na hanzarta tura makaman kakkabo makamai masu linzami 2 da kuma dakaru 400 zuwa Turkiya.

Ma'aikatar tsaro ta ce tura makaman na patriots da kuma sojojin wani bangare ne na wata rundunar kungiyar tsaro ta NATO wadda aikinta shi ne ta kare yankin kasar Turkiya daga yiwuwar harin Syria da makamai masu linzami.

Tuni dai Jamus da Holland sun amince da bayar da makaman kakkabo makamai masu linzamin 2 da kuma jumlar dakaru fiye da 700 tsakaninsu.

Rasha ta bayyana tura makaman da kuma sojojin a matsayin wani abun da bai taimakawa, tana mai karawa da cewar warware rikicin zai yiwu ne kawai tsakanin bangarorin dake adawa da juna a Syria.

Tun farko dai Rashar ta musanta cewar an samu wani sauyi a manufarta kan Syria, dukkuwa da lafazin wani babban Jami'in Diplomasiya wanda ya fada jiya cewar mai yiwuwa yan adawa su samu nasara kan Shugaba Bashar Al Assad.

Sanarwar da mataimakin ministan harkokin wajen Rashar ya bayar ta kasance babban labari a kasashen yamma, to amma gidajen TV na Rasha ba su bayar da rahoto kanta ba.

A halin yanzu ma'aikatar harkokin waje ta ce ya yi magana ne kawai dangane da ra'ayoyin yan adawar Syria.

Sai dai kuma wakilin BBC a Moscow ya ce kalaman na Mr Bogdanov za su iya zama wata alama ta ainihin abinda ake tunani ne a Rasha -- wadda take daya daga cikin kawaye mafiya muhimmanci ga Shugaba Assad.

Karin bayani