BBC navigation

DRC: 'Yan tawaye sun janye daga Goma

An sabunta: 1 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 14:40 GMT

'Yan tawayen jamhuriyar dimukradiyyar Congo sun soma janyewa daga birnin Goma da suka kwace iko da shi kwanaki goma da suka gabata.

An dai ga 'yan tawayen na kungiyar M23 a cikin manyan motocin daukar kaya suna fita daga birnin na Goma, ta hanyar da take zuwa garin Kibumba, inda 'yan tawayen zasu kasance bisa yarjejeniyar da aka cimma a Kampala babban birnin Uganda.

Ranar Jiya juma'a ma 'yan sandan Congon kusan dari hudu sun isa birnin na Goma domin dawo da doka da oda a wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma bisa jagorancin wasu shugabannin kasashen Afurka.

Yarjejeniyar da aka cimma a birnin Kampala babban birnin Uganda dai ta tanadi janyewar 'yan tawayen daga birnin na Goma.

Ana dai zargin Rwanda da tallafawa 'yan tawayen, sai dai Rwandan ta sha musanta wannan zargi.

Tun dai daga lokacin da 'yan tawayen suka juya baya ga rundunar sojan Congon cikin watan Aprilu, kimanin mutane miliyan daya ne suka tsere daga muhallinsu

Yankin da wannan lamari ke faruwa dai yana da dimbin arzikin ma'adinai, amma kuma an shafe shekaru ana tashin hankali a yankin.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.