BBC navigation

Dokar hukunta masu tuƙin ganganci ta soma aiki a Kenya

An sabunta: 1 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 18:24 GMT
Kenya

Masu tuƙin ganganci zasu soma fuskantar hukunci a Kenya

Sabuwar dokar da ake taƙaddama akanta akan tuƙin ganganci ta soma aiki a ƙasar Kenya yau, inda direbobi zasu fuskanci tsauraran hukunci da suka haɗa da hukuncin ɗaurin rai da rai.

Direbobin motocin bos sun soma yajin aiki tun ranar alhamis a babban birnin ƙasar Nairobi saboda wannan doka

Mutane da dama sunce ba zasu iya biyan tarar da za a rinƙa cinsu ba

Amma gwamnatin ƙasar tace babu gudu ba- ja- da- baya a ƙoƙarin da take na rage yawan mace macen da ake samu akan tituna

A bara kaɗai, mutane fiye da dubu uku ne suka mutu a ƙasar a hatsararrukan mota

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.