BBC navigation

Shugaba Morsi ya karɓi kundin tsarin mulki a hukumance

An sabunta: 1 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 20:05 GMT
Shugaba Morsi na Masar

Shugaba Morsi ya karɓi kundin tsarin mulki

Shugaba Mohammed Morsi na Masar ya karɓi sabon daftarin kundin tsarin mulkin ƙasar a hukumance, a yayinda dubun dubatar masu ra'ayin Islama ke gudanar da zanga zanga domin nuna goyan bayansu gare shi

Ana tsammanin Mr Morsi zai rattaba hannu akan kundin, sannan ya bada sanarwar ranar da za a kaɗa ƙuri'ar raba gardama akan- sa

Jam'iyyarsa ta 'yan uwa musulmi ta shirya gagarumin gangami a yau domin maida martani ga zanga zangar da 'yan adawa su ka yi, inda suka zargi Shugaba Morsi da yiwa doka karen tsaye

Majalisar dake aikin rubuta daftarin kundin tsarin mulkin da 'yan uwa musulmi suka fi rinjaye a cikinta, ta dai gagauta kammala wannan aiki

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.