BBC navigation

Zanga-zanga: Pillay ta soki Shugaba Morsi

An sabunta: 1 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 08:19 GMT

Kwamishinar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay

kwamishinar Hukumar Kare Hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay ta soki shugaba Mohammed Morsi na Masar akan abubuwan da ya yi a kwanakin nan da suka tayar da wutar zanga-zangar kin jini gwamnati a kasar.

Sukar dai na zuwa ne yayin da ake cigaba da gudanar da zanga-zanga a tsakiyar birnin Alkahira domin nuna rashin amincewa da yadda aka gaggauta samar da sabon daftarin kundin tsarin mulkin kasar.

Kwamishinar ta ce karfin ikon da ya baiwa kansa da babu wata hukuma da zata iya sokewa ko da kuwa kotu ce, bai dace da dokokin kasashen duniya ba, kuma hakan zai iya haddasa tauye hakkin dan adam.

Mrs Pillay ta rubutawa shugaban Masar din takarda ne inda take gargadinsa da kada ya aikata kuskuren da tsohuwar gwamnatin kasar ta yi.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.