BBC navigation

An yiwa Mahmud Abbas gagarumar tarba

An sabunta: 2 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 14:43 GMT

Mahmud Abbas, jagoran Palasɗinawa

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya faɗawa dubun dubatar magoya baya a gabar yamma da kogin jordan cewar 'Kuna da ƙasa yanzu'.

An dai yiwa Mahmud Abbas gagarumar tarba ne bayan da ya dawo daga taron majalisar ɗinkin duniya a New York, inda aka kuɗa ƙuri'ar ɗaukaka matsayin Palaɗinun.

Sai dai ana cikin hakan ne yau lahadi, ministan kudi na Israila yace ba zai turawa Palasdinawan kudaden da Israilan ta tatattara masu ba a wannan watan, a matsayin wani martani ga daukaka matsayin Palasdinawan da Majalisar dinkin duniya tayi

Ministan yace a madadin haka za a yi amfani da kudaden wanda akai kiyasta cewar zasu kai kusan dala miliyan dari da ashirin, wurin biyan bashin da wani kamfanin samar da hasken wutar lantarkin Isra'ilan yake bin hukumomin Paladinawan

A ranar juma'a dai Isra'ilan ta sanar da cewa zata cigaba da shirinta na gina dubun dubatar gidaje a filayen Palasdinawa

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.