BBC navigation

Majalisar Dinkin Duniya ta saka wa M23 takunkumi

An sabunta: 1 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 08:34 GMT
Mayakan kungiyar M23

Mayakan kungiyar M23

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayarda umarni kakaba takunkumi kan wasu manyan kwamandojin sojin kungiyar 'yan tawayen M23 su biyu.

Ana zargin kwamandojin biyu wato Baudoin Ngaruye da Innocent Kaina ne da saka kananan yara aikin sojin da kashe wadanda suka tsere daga aikin.

A ranar jumu'a ne kwamitin ya bayarda umarnin kakabawa kwamndojin biyu na M23 haramcin tafiye-tafiye da kuma rufe asusun ajiyar su na banki.

Kwamitin yace dama ya riga ya bayarda umarnin kakaba irin wannan takunkumin kan jagoran soji na kungiyar ta M23 Sultani Mukenga.

Sanarwa

Wata sanarwa da kwamitin ya fitar ta ce Ngaruye wanda shi ne mataimakin mukenga shi ne ke da alhakin kashewa da kuma azabtarda wadanda suka tsere daga rundunar mayakan 'yan tawayen na Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango.

Yayin da shi kuwa Innocent Kaina ya sanya ido kan dauka da kuma horarda yara sama da 150 domin yin yaki a cikin mayakan kungiyar ta M23 wadda ke da goyon bayan Rwanda.

Tawayen kungiyar ta M23 dai ya barke ne a watan Aprilu a lardin Kivu mai arzikin ma'adinai.

A watannan 'yan tawayen suka kaddamarda wani babban farmaki kan dakarun gwamnati kuma suka kwace babban birnin lardin wato Goma, wanda har anzu suke rike dashi duk da yarjeniyar dakatarda wutarda da aka cima wadda a karkashinta ya kamata su janye daga garin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.