BBC navigation

Kasashe na bukin ranar yaki cutar kanjamau ta Duniya

An sabunta: 1 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 07:12 GMT

Shugaban Hukumar yaki da Cutar kanjamau ta Majalisar Dinkin Duniya, Michel Sidebe lokacinda ya ke gabatarda kundin rahoto kan yaki da cutar a duniya a birnin Geneva.

Assabar din nan ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunatarwa game da cutar kanjamau wato AIDs da kuma duba halin da wadanda suka kamu da ita ke ciki a wannan shekara.

Tun bayan bullar cutar kwayar cutar mai karya garkuwar jiki wato HIV, nuna kyama ga mutanen da ke dauke da ita ya zamo wata gagarumar matsala da ke matukar barazana ga kokarin yaki da wannan cutar musamman a kasashe masu taso wa.

Masana halayyar rayuwar dan adam na ganin cewar nuna kyamar ya fi saurin hallaka masu fama da cutar fiye da ita kanta larurar da suke fama da ita; ko da yake rahotanni na nuna cewar matsalar nuna kyamar ta na raguwa a sassan duniya daban-daban.

Taken bikin na bana dai shi ne 'Babu sababbin kamuwa da cutar HIV, babu sauran nuna kyama, babu sauran mutuwar sakamakon cutar kanjamau'

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.