BBC navigation

Shugaban Mali yana ziyara a Niger

An sabunta: 2 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 20:17 GMT

Issoufou Muhammadu, shugaban Niger

A jamhuriyar Nijar shugabannin kasashen Nijar Alhaji Issoufou Mahamadou dana Mali Diouncounda Traore, sun jaddada bukatarsu na ganin an yi amfani da karfin soja domin kwato yankin arewacin kasar Mali dake hannun kungiyoyin 'yan kishin addinin islama da wasu 'yan tawaye tun farkon wannan shekarar.

Haka kuma shugabannin biyu sun nuna rashin jin dadinsu dangane da jan- kafar da wasu kasashe dama majalisar dinkin duniya keyi dangane da kaddamar da harin

Shugabanin na Nijar da Mali sun bayyana hakan ne a yau din nan, a wajen wata ganawa da sukai a birnin Yamai.

Kasashen kungiyar ECOWAS dai sun amince da shirin aike soja fiey da dubu uku zuwa Mali.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.