BBC navigation

Za a yi zaben raba gardama a Masar-Morsi

An sabunta: 2 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 06:07 GMT

Shugaba Mohamed Morsi

Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi ya ba da sanarwa cewar za a gudanar da kuri'ar raba gardama a kan sabon daftarin tsarin mulkin kasar a ranar goma sha-biyar ga watan Disamba.

Mr Morsi ya yi kira ga dukkan 'yan kasar ta Masar su shiga zaben, yana cewa dole ne kasar ta yi maganin abinda ya kira wani tashin hankali.

Ya ce duk duniya sun sa wa kasar ido kan abinda ke faruwa.

A ranar Assabar, dubun-dubatar mutane magoya bayansa sun yi tarukan gangami a Alkahira da shauran wasu birane a kasar.

Masu adawa da shi kuwa wadanda ke zanga-zanga a dandalin Tahrir yau Lahadi sun shiga rana ta goma.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.