BBC navigation

An fara farfado da hanyoyin sadarwa a Syria

An sabunta: 2 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 06:12 GMT

Shugaba Assad na Syria

A Syria, an farfado da hanyoyin sadarwa na tarho da Internet a wasu sassan kasar bayan fara katsewar su a Ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce, hanyoyin sadarwar sun yanke ne a dalilin rashin samun kula.

A rana ta uku a jere sojojin gwamnatin Syriar sun ci gaba da kai hari a kan wasu yankuna dake kusa da birnin Damascus - wasu daga cikinsu unguwanni ne dake kusa da babban filin saukar jiragen sama.

Gidan talabijin na kasar ta Syria ya ce har yanzu filin jirgin saman a bude yake.

Kungiyar dake sa ido ga al'amurran kare hakkin dan adam ta Syria ta ce an kashe mutane dari da goma ranar Assabar a sassa daban-daban na kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.