BBC navigation

Gwmnatin Colombia za ta cimma yarjejeniya da FARC

An sabunta: 3 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 08:17 GMT

Colombia

Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos ya ce lallai ne gwamnati da 'yan tawaye na Kungiyar FARC su cimma yarjejeniyoyin farko daga nan zuwa watan Nuwamban badi.

Mr Santos yace kamata ya yi a kawo karshen shawarwarin zaman lafiyar da yanzu haka ke gudana a kasar Cuba cikin watanni masu zuwa; ba wai shekaru ba.

Shugaban kasar ya ba da sanarwar ne a yayin da kungiyar 'yan tawayen ta FARC ta ambata cewa tana rike da abin da ta kira fursunonin yaki abinda ya saba wa ikirarin su a can baya.

A can baya dai hukumomin Colombia sun yi watsi da duk wani shiri na musayar fursunonin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.