BBC navigation

Ban Ki-moon ya soki Isra'ila kan gina matsugunan Yahudawa

An sabunta: 3 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 07:44 GMT

Ban Ki Moon

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi gargadin cewa shirin Isra'ila na gina matsugunan yahudawa zai wargaza duk wata yiwuwar cimma yarjeniyar zaman lafiya da Palasdinawa.

Isra'ila ta ce ta yi shirin gina karin wasu gidaje dubu uku a kan wadanda dama ta gina, tana kuma fatan kara gina wasu domin ta hade matsugunan na yahudawa dake Gabar yamma da Kogin Jordan da gabashin birnin Kudus.

Kasar ta bayar da sanarwar shirin ne, a matsayin wani martani ga kuri'ar da aka kada a Majalisar Dinkin Duniya wadda ta daukaka matsayin Palasdinu zuwa 'yar kallo.

A taron mako na majalisar zartarwa Prime Ministan Israila Benjamin Netanyahu, ya yi fatali da sukar shirin yin matsugunan Yahudawan.

Gwamnatin sa kuma ta bada sanarwar cewa ba za ta mika kudaden shiga na haraji da ta tattara a madadin hukumar Palasdinawa ba.

Ministan kudi na Israila ya fada karara cewa, sun dauki matakin ne don mayar da martani bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta kada kuri'a da ta daga matsayin diplomasiyya na Palasdinu, wanda ya bata matsayin yar kallo a karon farko a majalisar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.