BBC navigation

'Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Borno

An sabunta: 3 ga Disamba, 2012 - An wallafa a 08:02 GMT

wasu makamai da aka kwace a Najeriya

Wasu mutane da ake zargin 'yan kishin Islama ne sun kashe wasu mutane da wasu ake zaton Kiristoci ne su goma a gidajen su dake arewa maso gabashin Najeriya.

Mazauna yankin sun ce gungun wasu mutane ne dauke da bindigogi da adduna suka rinka bi gida-gida suna kashe mutanen a garin Chibok.

An ce sun yi wa wasu mutanen yankan-rago, sannan suka cinna wa gidajen su wuta.

'Yan Sanda dai ko Sojoji ba su ce uffan ba kan batun, amma jami'ai sun yi zargin 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram suka kai harin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.