Sirikar Sarauniyar Ingila ta samu juna biyu

Yarima William da Gimbiya Catherine
Image caption Yarima William da Gimbiya Catherine

An bayar da sanarwar cewa mai dakin jikan Sarauniya Yerima William, wato Catherine ta samu ciki. Sanarwar da fadar ta fitar ta kara da cewa cikin na ta karami ne.

Wata sanarwa da aka fitar daga fadar Sarauniya na cewa cikin nata karami ne, kuma an kwantar da ita a asibiti bayan da ta fara laulayi.

A karkashin sabbin dokokin da ake shirin kafawa, jaririn da zata haifa, mace ko namiji, shi zai kasance na uku a jerin masu jiran gadon sarautar Birtaniyar, bayan Yerima William.

Saurauniya da sauran 'yan gidan sarautar Birtaniya sun bayyana farin cikinsu da jin wannan labari.